2019-12-25 10:12:29 cri |
Rahotanni daga Idabato dake zirin Bakassi na kasar Kamaru, na cewa cutar amai da gudawa ko kwalara, ta hallaka mutane 25 cikin watanni biyun da suka gabata. Jami'an kiwon lafiyar kasar sun ce wannan ne karo na 2 da suka ziyarci yankin, domin ba da jinya, sakamakon barkewar cutar.
Da yake karin haske ga manema labarai, jami'in lafiya daga yankin kudu maso yammacin kasar Ebongo Zacheus Naji, ya ce baya ga wadanda cutar ta hallaka, akwai kuma wasu mutanen 325 dake karbar magani a cibiyoyin kula da lafiya. Naji ya ce a halin yanzu, tawagar su ta kai ga shawo kan wannan yanayi.
Bugu da kari, Mr. Naji ya ce an samar da cibiyar musamman domin kula da masu fama da cutar ta kwalara, da tallafin hukumar lafiya ta duniya WHO, da kuma kungiyar ba da agajin jin kai ta Red Cross.
Majiyar kamfanin dillancin labarai na Xinhua dai ta tabbatar da cewa, mafi yawan wadanda ke kwance a asibitocin yankin na fama ne da gudawa.
Yankin Bakassi mai arzikin mai, na da yawan al'umma sama da 200,000. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China