2020-01-08 09:00:20 cri |
A kalla fararen hula 6 ne suka mutu yayin wani hari da mayakan 'yan ta'adda na Boko Haram suka kaddamar a daren ranar Litinin a yankin arewa mai nisa na jamhuriyar Kamaru.
Hukumomin yankin sun ce mayakan Boko Haram sun kaddamar da harin ne a yankunan Moudoukoua da Hitere, dukkansu daga yankin Mayo-Moskota. An kuma yi garkuwa da mutane 3, kamar yadda wasu mazauna yankin da suka bukaci a sakaye sunansu suka bayyana.
A baya bayan nan mayakan Boko Haram suna cin karensu babu babbaka a yankin arewa mai nisa na Kamaru dake makwabtaka da Najeriya da Chadi.
Ko da a makon jiya, mayaka masu ikirarin jihadi, sun kashe wasu kauyawa biyu a yankin Kolofata. A karshen watan Disamba, an kashe mutane 50, galibinsu masu kamun kifi ne a tafkin Chadi a yankin mai fama da rikici.
Rahoton da jami'an tsaro suka fitar ya nuna cewa, sama da mutane 2,000 ne suka mutu tun bayan da Boko Haram ta kaddamar da hare haren ta'addanci a yankin arewa mai nisa na kasar tun daga shekarar 2014.(Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China