Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin saman Najeriya sun lalata sansanin mayakan Boko Haram
2019-12-19 08:54:13        cri

Rahotanni daga Najeriya na cewa, sojojin saman kasar sun yi nasarar kawar da daya daga cikin sansanonin mayakan Boko Haram a jihar Borno dake yankin arewa maso gabashin kasar.

Mai magana da yawun rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) Ibikunle Daramola ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kwafenta a birnin Lagos, ya ce, harin da sojojin suka kaddamar ranar Litinin a yankin Ngoske dake dajin Sambisa karkashin shirin "Operation Rattle Snake" ya hallaka mayakan na Boko Haram da dama.

Daramalo ya ce, harin wani mataki ne da sojoji suke dauka a wasu wurare na musamnan a yankin arewa maso gabas da nufin karya lagon gyauron 'yan ta'addan, da ma hana su sakat ko kaddamar da hare-hare kamar yadda suka saba.

A cewarsa, sojojin sama za su ci gaba da hada kai da takwarorinsu na kasa, har sai sun ga bayan ragowar mayakan 'yan ta'addan baki daya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China