Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Najeriya sun murkushe harin Boko Haram
2019-11-19 19:06:04        cri

Rundunar sojojin Najeriya ta ce dakarun ta sun yi nasarar murkushe wani kwantan bauna, da mayakan Boko Haram suka yi musu a jiya Litinin.

Wata sanarwa da kamfanin dillanin labarai na Xinhua ya samu kwafin ta a Talatar nan, mai dauke da sa hannun kakakin rundunar sojin Aminu Iliyasu, ta ce dakarun sojojin suna aikin sintiri a yankin karamar hukumar Dikwa dake jihar Borno ne, lokacin da 'yan Boko Haram din suka far musu, nan take kuma sojojin suka mayar da martani.

Mayakan Boko Haram din sun kuma binne wasu ababen fashewa a hanyar sojojin ta zuwa kauyen Ala mai nisan kilomita 7 daga gari Marte, a wani mataki na tabbatar da sun hallaka su, to sai dai a cewar sanarwar, sojojin sun ja daga, inda suka fatattaki mayakan, wadanda da dama daga cikin su suka tsare da raunukan bindiga a jikin su.

Sanarwar ta kara da cewa, yanzu haka sojojin na bin sahun mayakan, wadanda suka tsare suka bar kayayyakin fada da suke dauke da su a yayin dauki ba dadin.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China