Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Najeriya sun ceto mutane 31 daga hannun mayakan Boko Haram
2019-12-09 20:10:44        cri

Rahotanni daga Najeriya na cewa, sojojin kasar sun yi nasarar ceto mutane 31 da mayakan 'yan ta'adda na Boko Haram suka yi garkuwa da su a karamar hukumar Bama ta jihar Borno dake yankin arewa maso gabashin kasar, yayin wani samame da suka kaddamar a yankin.

Da yake karin haske kan lamarin, kakakin sojojin dake yankin arewa maso gabashin Najeriya, Aminu Iliyasu, ya bayyana cewa, wadanda aka ceton sun hada da mata 14 da yara 17. Ya ce, sojojin sun yi nasarar ceto mutanen ne, bayan da suka yi musu kwanton bauna. Yayin samamen, sojojin sun kuma gano wani gungun mayakan, inda suka yi musayar wuta, lamarin da ya kai ga mutuwar mayakan da dama, kana wasu kuma suka arce da raunin harbin bindiga a jikinsu yayin bata kashin.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China