![]() |
|
2019-12-30 11:51:17 cri |
Kwamitin sulhun ya fada cikin wata sanarwa cewa, ayyukan ta'addanci sun kasance manyan abubuwan dake zama barazana ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa, kwamitin MDD ya jaddada bukatar hadin kan dukkan kasashen duniya wajen kawar da barazanar hare-haren ta'addanci.
Kana ya bukaci dukkan kasashen duniya su yi hadin gwiwa da gwamnatin kasar Somaliya da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki wajen binciko wadanda ke da hannu, da masu daukar nauyin ayyukan ta'addancin domin gurfanar da su a gaban shari'a.
Haka zalika kwamitin sulhun MDD ya sha alwashin daukar matakan tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaban kasar Somalia, sannan ya nanata cewa babu abin da zai sanyaya musu gwiwa wajen dakile hare haren ta'addancin.
Mutane 79 aka tabbatar da mutuwarsu kana wasu 149 sun samu raunuka a harin bam din da aka kaddamar a wajen binciken ababen hawa na jami'an tsaro a Mogadishu a ranar Asabar din da ta gabata. (Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China