Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mozambique ta sha alwashin samar da ilmi ga kananan yara a yankunan da rikici ya shafa
2020-01-07 09:52:01        cri

Hukumomin ilmi a kasar Mozambique sun ba da tabbacin cewa, babu wani yaro da za'a cire daga makaranta sakamakon rahotannin hare hare da ake samu a shiyyoyin tsakiya da kuma arewacin kasar.

Babban daraktan cibiyar bunkasa ilmi na kasar Ismael Nheze ya ce idan akwai yaran da aka dauke su daga wata shiyya zuwa wata, gwamnati za ta samar da wani tsarin ilmantar da su a wadannan yankunan da suke zaune a halin yanzu.

Daraktan ya bayyana hakan ne ga manema labarai game da shirye shiryen fara sabuwar shekarar karatu ta wannan shekarar, ya ce cibiyar ilmin kasar tana aiki tare da sauran hukumomin ilmi na larduna da gundumomi domin duba yadda za'a ceto ilmin kananan yaran da rikicin hare hare suka shafe su.

Nheze ya ce, gwamnati tana aiki da abokan hulda wajen samar da tantuna da za'a yi amfani da su na wucin gadi a matsayin ajujuwan karatu domin yaran da rikicin ya shafa su ci gaba da halartar darrusa.

Ana sa ran sabuwar shekarar karatun za ta fara daga watan Fabrairu kuma za'a raba littattafai ga dukkan gundumoni, ciki har da yankunan da hare haren suka shafa.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China