Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Habasha na fatan karfafa alaka da Sin a fannin raya ilimin manyan makarantu
2019-09-09 09:29:53        cri

Ministan ma'aikatar kimiyya da ilimin manyan makarantu na kasar Habasha Hirut Woldemariam, ya bayyana aniyar kasar sa, na karfafa hadin gwiwa da kasar Sin, a fannin raya ilimin gaba da sakandare, a gabar da Habashan ke kokarin inganta sha'anin ilimi a manyan makarantun ta.

Ministan ya bayyana hakan ne, yayin da yake tsokaci, a bikin nune nunen sashen ilimin kasar Sin na bana da ya gudana ranar Lahadi a birnin Addis Ababa, fadar mulkin kasar, taron da ya samu halartar manyan jami'o'in kasar Sin 31.

Mr. Woldemariam, ya ce kasashen biyu sun jima suna hadin gwiwa da cudanya da juna a sassa daban daban, kuma fannin ilimi na kan gaba, cikin fannonin da Habasha ke fatan ci gaba da hadin gwiwa da Sin.

A nasa tsokaci yayin baje kolin, jakadan Sin a Habasha Tan Jian, ya ce hadin gwiwa a fannin raya ilimi, na sahun gaba cikin sassa da Sin ke baiwa muhimmanci, yayin da take mu'amala da kasashen nahiyar Afirka.

A cewar sa, bunkasa kwarewar ma'aikata, muhimmin sashe ne na ayyukan dake kunshe cikin shawarar ziri daya da hanya daya, wadda ake aiwatarwa karkashin lemar dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka ta FOCAC. Jakadan ya ce, baya ga samar da kwarewa, manufar ta kuma kunshi karfafa dankon zumunta tsakanin al'ummun sassan biyu. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China