Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin Alibaba ya bude shirin horas da 'yan kasuwar Habasha
2019-12-19 10:23:24        cri

Makarantar nazarin harkokin kasuwanci ta Alibaba tare da hadin gwiwar ma'aikatar kirkire-kirkire da fasahar kere-kere ta kasar Habasha, za su bude wani shirin horas da 'yan kasuwa da masu kamfanoni na farko daga kasar ta Habasha a watan Maris na shekarar 2020.

A watan da ya gabata ne dai, katafaren kamfanin cinikayya ta yanar gizo na kasar Sin, ya sanya sannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna da kasar Habasha, inda zai kafa wani dandalin cinikayya ta yanar gizo na duniya (eWTP), matakin da aka yi imanin cewa, zai canja tsarin tattalin arziki kasar zuwa na zamani.

Manufar shirin na kwanaki goma da za a gudanar a hedkwatar kamfanin Alibaba dake birnin Hangzhou na kasar Sin ita ce, koyar da 'yan kasuwa da shugabannin kamfanoni fasahar zamani, ta yadda za su yi nasara a harkokinsu na kasuwanci.

Da yake jawabi ga halarta taron da aka tattauna kan sassa masu zaman kansu da hada-hadar cinikayya ta yanar gizo makon da ya gabata a Addis Abba, babban birnin Habasha, karamin ministan cinikayya da masana'antu na kasar Habasha, Mesganu Arga Moach, ya yaba dandalin na eWTP kan rawar da ya taka, wajen ba da damar cin gajiya daga kasuwannin duniya da hada kanana da matsakaitan masana'antun Habasha waje guda

Ministan ya kuma bayyana dandalin cinikayyar yanar gizo na duniya na kasar na baya-bayan nan, a matsayin na biyu a Afirka bayan na Rwanda, zai kuma baiwa Habashan damar samar da hidimomi da matakai na zamani, cinikayya a kan iyakokin kasashe ta hanyar mayar da hankali kan kanana da matsakaitan masana'antu.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China