Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministan Habasha ya yaba taimakon da Sin take bayarwa a fannin kimiyar sararin samaniya
2019-12-16 09:53:51        cri

Ministan kirkire-kirkire da fasahar kere-kere na kasar Habasha Getahun Mekuria, ya yaba da hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Habasha a fannin raya kimiyar sararin samaniya.

Da yake karin haske yayin zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Mekuria ya bayyana cewa, ma'aikatarsa ta yi hadin gwiwa da takwararta ta kasar Sin don horas da injiniyoyin zirga-zirgar sararin samaniya na kasar Habasha tare da taimakawa kasar wajen harba tauraron dan-Adama dinta na farko zuwa sararin samaniya.

Mekuri, ya bayyana cewa, tuni ma masanan kasar Sin suka taimaka wajen horas da injiniyoyin Habasha guda 20 a kasar Sin da ma gida Habasha. Ana sa ran wadannan injiniyoyi da kasar Sin ta horas, za su taka muhimmiyar rawa wajen kula da tauraron dan-Adam din kasar ta Habasha na farko.

Kasashen Sin da Habasha dai, sun kulla alaka a fannoni da dama, wannan ne ma ya sa kasar Sin za ta taimakawa Habashan wajen harba tauraron dan-Adam din ta na farko a ranar 20 ga wannan wata daga nan kasar Sin, za kuma a rika sarrafa shi a cibiyar kula da tauraron dan-Adam na kasar dake tsaunin Entoto mai tsayin mita 3,200, dake wajen birnin Addis Ababa, babban birnin kasar

Da zarar ya fara aiki, ana sa ran tauraron dan-Adam din ya taimakawa kasar adana kimanin kudin kasar birr miliyan 350, kwatankwacin dala miliyan 11 a shekara, kudaden da halin yanzu take kashewa wajen karbar bayanai daga taurarin dan-Adam na wasu kasashe.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China