Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kaiwa shingen tsaro dake kusa da gidan tsohon shugaban Najeriya hari
2019-12-25 09:16:32        cri

Rahotanni daga jihar Bayelsa a kudu maso kudancin Najeriya, na cewa wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba, sun farwa wani shingen tsaro dake kusa da gidan tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan, harin da ya sabbaba rasuwar soja daya, da kuma jikkatar wani sojan na daban.

An ce dai 'yan bindigar sun kaddamar da harin ne a Otuoke, mahaifar tsohon shugaban da sanyin safiyar jiya Talata, tuni kuma shugaban kasar mai ci Muhammadu Buhari, ya gabatar da sakon jaje ga Mr Jonathan.

Wata sanarwa da mai tallafawa tsohon shugaban kan harkokin watsa labarai Ikechukwu Eze ya fitar, ta ce 'yan bindigar sun isa shingen tsaron ne cikin wasu kananan jiragen ruwa masu injiyi guda 5, kuma mai yiwuwa sun so ne su kwace jirgin ruwa mai dauke da bindiga, da ma'aikatan tsaron wurin ke amfani da shi.

To sai dai kuma sanarwar ta ce burin maharan ya ci turo, domin kuwa sojojin dake aiki a lokacin sun yi musu ruwan wuta, wanda hakan ya tilasa musu tserewa.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China