Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Iran ta bayyana tsananta matsin lamba da Amurka ke mata a matsayin yunkurin rusa gwamnatin kasar
2019-09-15 16:04:36        cri

Mataimakin shugaban kasar Iran na 1, Eshaq Jahangiri, ya ce Amurka na yunkurin rusa gwamnatin kasar ne ta hanyar tsananta matsa mata lamba.

Kamfanin dillancin labarai na Iran IRNA, ya ruwaito Eshaq Jahangiri na cewa, Washington, a matsayinta na daya daga cikin kasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar nukiliyar kasar, ta yi gaban kanta wajen janyewa daga yarjejeniyar a bara kuma ta kaddamar da yaki kan Iran ta hanyar sake kakaba mata takunkumin tattalin arziki.

A watan Mayun shekarar 2018 ne shugaban Amurka Donald Trump, ya janye kasarsa daga yarjejeniyar tare da kakabawa Tehran takunkumi.

Fadar White House ta Amurka dai, ta lashi takobin tsananta matsawa Iran lamba domin matsa mata hawa teburin sulhu da sanya hannu kan sabuwar yarjejeniyar nukiliya, da za ta takaita shirin nukiliya da tasirin Iran a shiyyar, abun da Iran din take kin amincewa da shi. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China