Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kolin Iran ya bukaci a haramta duk wata tattaunawa da Amurka
2019-11-04 10:13:04        cri

Shugaban kolin kasar Iran Ayatollah Ali Khamenei ya bayyana a jiya Lahadi cewa, ya kamata a haramta duk wata tattaunawa tsakanin kasar da Amurka domin toshe duk wata kofar da Amurka za ta samu yiwa kasar kutse.

An jiyo Khamenei yana bayani ta gidan talabijin din Press TV yana cewa, haramcin tattaunawa da Amurka al'amari ne mai dadadden tarihi, hakan zai toshe duk wata kafa da makiya za su samu yin kutse ga kasar, hakan zai kara bayyanawa duniya irin karfin da Iran din ke da shi, kana zai bayyanawa duniyar irin kuskuren da Amurkar ke tafkawa.

Ya yi tsakacin ne kwana guda gabanin bikin murnar zagayowar ranar kwace ofishin jakadancin Amurkar da daliban Iran suka yi a Tehran.

A ranar 4 ga watan Nuwambar shekarar 1979, daliban kasar Iran suka mamaye ofishin jakadancin Amurka, inda daliban suka tsare jami'an ofishin jakadancin Amurkan na tsawon kwanaki 444.

A shekarar 1980, Amurka ta yanke huldar diplomasiyya da Iran.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China