Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Iran ta sanar da daukar mataki na hudu na kin martaba yarjejeniyar nukiliyarta
2019-11-06 10:17:05        cri

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya sanar a ranar Talata cewa, kasarsa za ta dauki mataki na hudu na kin martaba yarjejeniyar nukiliyar kasar da aka cimma a shekarar 2015, kamfanin dillancin labarai na IRNA ya ba da rahoton.

An jiyo Rouhani yana cewa, "Daga gobe, Iran za ta fara tura gas zuwa cibiyar nukiliyar kasar dake Fordow".

Ya kara da cewa, hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa IAEA, tana sane da sabon matakin da Iran za ta dauka kuma za ta ci gaba da sanya ido kan harkokin nukiliyar ta Iran.

Shugaban kasar Iran ya ce, Tehran a shirye take ta mutunta yarjejeniyar nukiliyar ta shekarar 2015 idan bangarorin da abin ya shafa su ma sun tabbatar da aniyarsu kan batun.

Rouhani ya ce, Iran za ta dakatar da aikin tura gas zuwa cibiyar hada nukiliyarta idan har bangarorin suka aiwatar da yarjejeniyar don kare moriyar Iran kamar yadda yarjejeniyar ta tanada.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China