Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na fatan za a cimma manyan nasarori a shekarar jagorancin BRICS da Rasha ta fara
2020-01-03 19:35:25        cri

Tun daga ranar 1 ga watan nan na Janairu, kasar Rasha ta karbi ragamar jagorancin kungiyar BRICS a hukumance, za kuma ta shigar da na ta dabarun ci gaba, domin bunkasa hadin gwiwar sassan kungiyar.

Da yake tsokaci game da hakan, yayin taron manema labarai da ya gudana a Juma'ar nan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Geng Shuang, ya ce Sin na fatan ganin an samu sabbin ci gaba a wannan kungiyar ta BRICS a bana, karkashin jagorancin Rasha.

Geng Shuang ya ce BRICS na kunshe da kasashe mambobi dake samun saurin bunkasar tattalin arziki da tasiri a duniya, suna kuma fadada hadin gwiwar su da sauran kasashe masu tasowa. Ya ce a 'yan shekarun baya bayan nan, kasashe mambobin BRICS, sun kara fadada tasirin su a fage na tattauna batutuwan kasa da kasa, sun kara dunkulewa, sun kuma zurfafa hadin kai da fada a ji.

Jami'in ya kara da cewa, a wannan yanayi da ake ciki, dabarun da kasashe mambobin BRICS suka bi, wajen tunkarar sauye sauyen duniya, da rawar da suka taka wajen bunkasa ci gaban duniya, sun zama wani abu dake jan hankalin kasa da kasa. Ya ce Sin za ta goyi bayan shugabancin Rasha, da ci gaba da martaba alakar kut da kut tsakanin su, da ma sauran kasashe mambobin kungiyar, za ta kuma agaza wajen ganin taron kungiyar na birnin St. Petersburg ya cimma nasara. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China