Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firayin ministan Sin ya gana da mataimakin shugaban Afirka ta kudu
2019-10-29 20:20:16        cri

Yau Talata a nan birnin Beijing firayin ministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da David Mabuza, mataimakin shugaban kasar Afirka ta kudu wanda ke ziyarar aiki a nan kasar Sin, inda Li ya bayyana cewa, kasar Sin tana son kara karfafa fahimtar juna tsakaninta da Afirka ta kudu, domin ingiza hadin gwiwa da cudanyar al'adu tsakanin sassan biyu, tare kuma da ciyar da huldar dake tsakanin Sin da Afirka ta kudu da kuma Sin da kasashen Afirka gaba yadda ya kamata.

Kana Li Keqiang ya yi nuni da cewa, kasar Sin tana son kara karfafa tattaunawa tsakaninta da Afirka ta kudu kan harkokin kasa da kasa da na shiyya shiyya, haka kuma tana son kara karfafa hadin gwiwa tsakaninta da Afirka ta kudu bisa tsarin MDD da kuma kungiyar BRICS, ta yadda za su kiyaye moriyar kasashe masu tasowa da kuma kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin duniya.

A nasa bangare, Mabuza ya bayyana cewa, yanzu haka huldar dake tsakanin kasarsa da kasar Sin ta samu ci gaba daga dukkan fannoni, kasarsa tana jinjinawa kasar Sin saboda babban sakamakon da ta samu yayin da take kokarin raya kasa, a don haka tana son koyon fasahohin da kasar Sin ta samu, kuma za ta yi kokari domin zurfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu tare kuma da ingiza ci gaban huldarsu yadda ya kamata.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China