![]() |
|
2019-10-28 19:11:59 cri |
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya sanar a yau Litinin cewa, mataimakin shugaban kasar Afirka ta kudu David Mabuza, zai kawo ziyarar aiki kasar Sin daga ranar 30 ga watan Oktoba zuwa 3 ga watan Nuwamba, bisa gayyatar takwaransa na kasar Sin Wang Qishan.
Geng ya ce, yayin ziyarar, ana sa ran Wang da Mabuza za su jagoranci zama na bakwai na hukumar raya hadin gwiwar kasashen biyu. (Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China