Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yan sandan Morocco sun gano tan 16.2 na tabar wiwi
2019-12-31 09:54:31        cri

Jiya Litinin hukumar tsaron kasar Morocco ta bayar da wani rahoto cewa, 'yan sandan kasar sun gano tan 16.2 na tabar wiwi a tashar ruwan Tangier Med dake arewancin kasar.

Rahoton ya bayyana cewa, 'yan sandan sun gano tabar wiwin ce a cikin wata babbar mota bisa taimakon jami'an hukumar kwastam, kuma sun cafke direban motar mai shekaru 35, 'dan asalin kasar.

Ana shuka tabar wiwi a wasu yankunan kasar ba bisa ka'ida ba, a cikin shekaru sama da goma da suka gabata, 'yan sandan kasar sun kara daukar matakai domin yaki da wannan matsala, inda suka yi nasarar gano tabar wiwi mai yawan gaske, rahotannin sun bayyana cewa, ana sayar da yawancin tabar wiwin da ake samarwa a Morocco a kasashen Turai ta barauniyar hanya.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China