Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Morocco ta ceto bakin haure 249 daga gabar ruwan arewacin kasar
2019-05-28 10:23:26        cri

Rundunar sojojin ruwan kasar Morocco, ta ceto wasu bakin haure da suka fito daga kasashen yankin kudu da hamadar Sahara su 249 daga gabar ruwan kasar ta arewaci, ciki hadda mata da yara kanana.

Rundunar sojin ruwan kasar ta bayyana hakan ne a jiya Litinin, inda ta ce tsakanin ranekun 25 zuwa 26 ga watan nan na Mayu, dakarun ta masu tsaron bakin teku, sun ceto mutanen daga wasu kwale kwale na roba, wadanda ake amfani da su a yunkurin tsallaka tekun Meditireniya zuwa yankunan Turai ta barauniyar hanya.

Rahoranni na cewa, tuni aka kai mutanen tashoshin ruwan kasar na biranen Ksar-Sghir, da Al-Hoceima da kuma Nador.

Gwamnatin Morocco ta ce a bana kawai, ta samu nasarar dakile yunkurin bakin haure 30,000 na tsallakawa Turai ta tekun Meditireniya, yayin da adadin yunkurin tsallaka tekun a bara ya kai sama da 80,000.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China