2019-12-16 11:09:06 cri |
Jami'an tsaron kasar Morocco sun cafke wani mutum da suke zargin yana da alaka da kungiyar masu da'awar kafa daukar Islama ta IS.
Mutumin mai shekaru 41, an kama shi ne a ranar Asabar a birnin Meknes. Ana zargin mutumin da yunkurin shirya harin kunar bakin wake, hukumar bincike game da shari'a, wato hukumar tattara bayanan sirri ta kasar Morocco ce ta bayyana a cikin wata sanarwa.
Sanarwar ta kara da cewa, an kwace dukkan wasu na'urori da wasu takardu dake da nasaba da shirin hada ababen fashewar daga wajen mutumin.
A binciken da aka gudanar, an gano cewa, mutumin da ake zargin yana da hannu wajen yada manufofin tsattsauran ra'ayi na kungiyar IS.
A cewar sanarwar, za'a gurfanar da wanda ake zargin gaban shari'a da zarar an kammala binciken da ofishin gudanar da binciken laifuka na kasar ke gudanarwa.(Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China