Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Iraki ta soki hari ta saman da Amurka ta kai sansanin PMF
2019-12-31 09:50:36        cri

Jiya Litinin gwamnatin kasar Iraki ta fitar da wata sanarwa, inda ta soki Amurka kan hari ta sama da sojojinta suka kai kan sansanin dakarun 'yan shi'a na PMF na kasar dake kan iyakar Iraki da Syria.

Hukumar kiyaye tsaron kasar Iraki ta kira wani taron gaggawa karkashin jagorancin firayin ministan gwamnatin wucin gadin kasar Abdul-Mahdi jiya, daga baya ta fitar da wata sanarwa cewa, gwamnatin kasar ta soki harin da Amurkar ta kai, tana ganin cewa, matakin da Amurka ta dauka ya keta ikon mulkin kasar Iraki, saboda ta dauki matakin ne ba tare da samun amincewar gwamnatin Iraki ba, kana harin ya sabawa ka'idar da kawancen kasa da kasa na yaki da kungiyar IS karkashin jagorancin Amurka ya tsara.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China