Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Fashewar wani abu a sansanin soji dake Baghdad ta yi sanadin mutuwar mutum 1 da raunatar wasu 29
2019-08-13 14:42:15        cri

Akalla mutum 1 ya mutu, wasu 29 kuma sun ji rauni, biyo bayan fashewar wani abu a wani sansanin adana makaman soji dake kudancin Baghdad, a jiya Litinin.

Kakakin ma'aikatar lafiya ta kasar Iraq Sayf al-Badr, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, an kwantar da wasu daga cikin wadanda suka jikkatan a asibitocin al-Yarmouk da al-Mahmoudiyah, wadanda ke da nisan kilomita 30 daga kudancin Baghdad.

Ya kara da cewa, yawancin wadanda lamarin ya rutsa da su, ba su ji munanan raunika ba, kuma tuni aka sallami wasu daga cikinsu.

Sai dai kakakin bai yi karin bayani game da wadanda suka jikkata daga cikin jami'an tsaron dake cikin sansanin ba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China