Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wadanda suka mutu a rikicin masu zanga zangar Iraqi sun kai 99
2019-10-06 17:12:13        cri

Wani mamban hukumar kare hakkin bil adama ta Iraqi ya bayyana a jiya Asabar cewa, adadin mutanen da suka rasu a rikicin masu bore na kwanaki biyar a Bagadaza, babban birnin kasar Iraqi da sauran lardunan kasar ya kai mutane 99, kana wasu mutanen kusan 4,000 sun samu raunuka.

Ali al-Bayati, mamban hukumar kare hakkin dan adam mai zaman kanta ta kasar Iraqi (IHCHR), ya fadawa 'yan jaridu cewa, yawan mutanen da suka mutu a zanga zangar da ta rikide zuwa tashin hankali a kwanaki biyar a Bagadaza da sauran larduna ya kai mutane 99, wanda ya hada har da jami'an tsaro.

Ya ce, sama da mutane 3,991 ne suka samu raunuka, galibin masu zanga zangar, sun tada rikici ne a birnin Bagadaza da sauran birane, a cewar al-Bayati.

Al-Bayati ya kara da cewa, an hallaka masu zanga zanga biyar a kusa da babban kantin al-Nakheel dake kan titinin Palestine tun a farkon ranar Asabar a gabashin Bagadaza, a yayin da jami'an tsaro sun yi amfani da alburusai da hayaki mai sa hawaye don tarwatsa gangamin masu boren.

Ya kara da cewa, zanga zanga a birnin Diwaniyah, helkwatar lardin al-Qadsiyah, dake kudancin Iraqi ta yi sanadiyyar raunata masu bore 13, a yayin da jami'an tsaro suka bude wuta da nufin tarwatsa masu zanga zangar wadanda ke yunkurin kutsawa ginin gwamnati na hukumar gudanarwar lardin.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China