![]() |
|
2019-12-11 19:28:24 cri |
Yau mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana cewa, kasar Sin tana adawa da Amurka saboda tana yunkurin kaucewa alhakinta kan kwance damara ta hanyar fakewa da batun dake shafar kasar Sin.
Rahotanni sun ce, sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya yi shawarwari da takwaransa na Rasha, daga baya ya gaya wa manema labarai cewa, ya kamata a kara fadada aikin kwance damara, misali a kasar Sin.
Hua Chunying ta kara da cewa, ya dace Amurka wadda take da makaman nukiliya mafiya inganci a duniya ta dauki matakin kwance damara, tare kuma da rage makaman nukiliyarta, ta yadda za ta shatawa sauran kasashe sharadi saboda su shiga tattaunawar rage makaman nukiliya tsakanin bangarori da dama.(Jamila)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China