Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin ya ce wanzar da zaman lafiya babban aiki ne dake gaban Sudan ta kudu
2019-12-18 14:38:27        cri

Wakilin kasar Sin ya bayyana cewa, aikin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali shi ne muhimmin al'amari da ya kamata Sudan ta kudu ta baiwa fifiko a kasar wacce rikici ya daidaita.

Wu Haitao, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, ya bayyana wa kwamitin sulhun MDD cewa, aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya, wacce dukkan bangarorin Sudan ta kudun suka rattaba hannu kanta a bara, shi ne muhimmin matakin da zai iya warware takaddamar siyasar kasar ta shiyyar Afrika.

Sudan ta kudu ta tsunduma cikin yakin basasa ne tun a watan Disambar shekarar 2013, bayan da shugaban kasar Salva Kiir ya tube mataimakinsa Riek Machar daga mukaminsa, lamarin da ya haddasa yaki tsakanin bangarorin dakarun sojoji dake biyayya ga tsagin shugabannin biyu.

Yarjejeniyar da aka cimma matsaya kanta ta tanadi matakan tabbatar da zaman lafiya wanda ya kunshi wa'adin rikon kwarya da kuma kafa gwamnatin hadin kan kasa.

A cewar mista Wu, ya kamata al'ummomin kasa da kasa, musamman kwamitin sulhun MDD, su bayar da babban taimako game da mayar da hankali wajen tabbatar da ganin an aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin dukkan bangarorin kasar.

Wakilin na Sin ya ce, dangane da wannan batu, ya kamata bangarorin su martaba shugabancin gwamnatin Sudan ta kudu yayin da dukkan bangarorin kasar ke kokarin sauke nauyin dake bisa wuyansu wajen aiwatar da yarjejeniyar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China