Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi zai halarci babban taron MDD karo na 74
2019-09-16 19:12:33        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Sin Hua Chunying, ta ce babban dan majalissar zartaswar Sin, kuma firaministan kasar Wang Yi, zai halarci taron mahawara na shekara shekara na MDD ko UNGA a ranar Talata mai zuwa.

Taron na wannan karo wanda shi ne na 74, zai gudana ne tsakanin ranekun 17 zuwa 30 ga watan Satumba. Ana kuma fatan gudanar da babban taron mahawarar ne a ranar 24 ga wata.

A cewar Hua, a matsayin sa na wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, Wang zai halarci taron sauyin yanayi, da babban taron dandalin siyasa na MDDr game da aiwatar da manufofin ci gaba mai dorewa ko SDGs a takaice, da ma sauran batutuwa na hadin gwiwar sassan biyu.

Kaza lika Mr. Wang zai gabatar da matsayar kasar Sin, game da ci gaba da aiki tare da kasashe mambobin MDD, wajen tabbatar da cudanyar bangarori daban daban, da kare kudurori da dokokin MDD, tare da fadada sadarwa da tsare tsare, tare da sauran kasashe da hukumomin kasa da kasa.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China