Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin saman Najeriya sun kai hari kan wurin da Boko Haram ke taro
2019-12-17 09:05:52        cri

Rundunar sojojin saman Najeriya ta bayyana cewa, wani hari da dakarunta suka kai ta sama, ya yi nasarar fadawa kan wurin da mayakan Boko Haram ke taro, tare da kashe mayakan da dama a wani yanki na tafkin Chadi a jihar Borno dake yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Wata sanarwa da rundunar sojojin saman ta rabawa manema labarai a jiya Litinin, ta bayyana cewa, mayakan suna kokarin sake haduwa ne, inda suke ganawa a wani gini dake tsakiyar Kollaram a jihar ta Borno, inda aka tura jiragen yaki wurin ranar Asabar don su fatattake su.

Rundunar ta ce, sojojin sun kai harin ne, bayan samun bayanan sirri, wannan wani bangare ne na matakan da sojojin suke dauka, na kawar da gyauron kungiyar mayakan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China