Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Iraqi zai yi murabus sakamakon dambarwar siyasar kasar
2019-12-27 10:22:45        cri
Shugaban kasar Iraqi Barham Salih ya sanar cewa, a shirye yake ya mika takardar yin murabus daga shugabancin kasar ga majalisar dokokin kasar, bayan da ya ki amincewa da nada Asad al-Eidani a matsayin firaministan kasar, gidan talabijin din kasar Iraqi ne ya ba da rahoton.

A cikin wasikar da ya aikewa shugaban majalisar dokokin kasar Mohammed al-Halbousi, Salih ya yi watsi da nada al-Eidani wanda gamayyar wasu kungiyar suke bukata, kungiyar wanda masu rinjaye a zaben majalisar dokokin kasar na 2018 suka kafa, kamar yadda tashar Iraqiya ta bada rahoton.

A wata wasika, wacce kafar yada labaran kasar ta wallafa ta ce, matsayar Salih game da nadin mukamin tamkar keta dokokin kasa ne, don haka a shirye yake ya mika takardar sauka daga kujerar shugabancin kasar.

Salih ya kuma kara da cewa, masu zanga zangar kasar ba sa maraba da nadin al-Eidani.

A cikin wasikar tasa, shugaban kasar Iraqin ya bayyana cewa, tilas ne manufofin siyasar kasar da na majalisar dokokin kasar su dace da muradun al'ummar kasar, domin cimma nasarar wanzar da zaman lafiya da tsaro, da tabbatar da shugabanci na gari wanda yayi daidai da muradun jama'ar kasar. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China