Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamaru ta soki lamirin shugaban Amurka game da batun rikicin 'yan awaren kasar
2019-11-19 20:40:32        cri

Gwamnatin Kamaru ta soki lamirin shugaban kasar Amurka Donald Trump, bisa zargin kasar da keta hakkokin al'ummun dake zaune a yankunan da ake magana da Turancin Ingilishi.

Cikin wata wasika da ya aike wa majalissar dokokin Amurka a ranar 31 ga watan Oktoba, shugaba Trump ya ce, nan gaba kadan, zai tsame kasar Kamaru daga jerin kasashen da suka cancanci cin gajiya daga tallafin Amurka karkashin shirin AGOA, yana mai cewa mahukuntan kasar na keta hakkokin bil Adama da kasa da kasa suka amincewa. Shugaba Trump ya ce sojojin Kamaru na hallaka al'umma ba tare da yi masu shari'a ba, ana kuma tsare mutane, a azabtar da su a yankunan arewa maso yammaci, da kudu maso yammacin kasar.

To sai dai kuma a bangaren gwamnatin Kamaru, kalaman na shugaban Amurka cike suke da ban mamaki, kasancewar ko kadan, ba su tabo irin ta'addanci da gwamnatin Kamarun ke cewa 'yan awaren na aikatawa ba.

Yayin wani taron manema labarai, kakakin gwamnatin kasar Emmanuel Rene Sadi, ya ce abun mamaki ne ganin yadda ko kadan, shugaban na Amurka bai tabo batu, kan irin ta'asar da 'yan awaren ke tafkawa ba a wadannan yankuna biyu.

Ya ce sam bai dace a nunawa dakarun sojin kasar tsana ba, kasancewar ayyukan su sun hada da na tsaron kasa, da kare rayuka da dukiyoyin al'ummun dake zaune a wadannan yankuna, matakin dake amfanar daukacin mazauna yankunan. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China