2019-11-23 16:17:20 cri |
Shugaban kasar Kamaru, Paul Biya, ya yi kira da a kara zage damtse domin kara raya tattalin arzikin kasashen kungiyar raya yankin tsakiyar nahiyar Afrika.
Paul Biya, ya bayyana yayin bude taron shugabannin kasashe mambobin kungiyar jiya a birnin Yaounde cewa, sauye-sauyen farashin kayayyakin da ake sarrafawa na ci gaba da tasirin a kan tattalin arzikin kasashen, don haka akwai bukatar kara baza komar tattalin arziki fiye da baya. Yana mai cewa kalubalen tsaro na ci gaba da matsawa harkar hada hadar kudi a yankin.
Ya ce buri guda da suke da shi, shi ne gaggauta samun ci gaba don magance halaltattun bukatun al'ummominsu, musammam na matasa a fannin samun ayyukan yi.
Shugaba Paul Biya ya kara da cewa, ci gaban kungiyar ya tsaya ne kan kaso 1.8 a bara, yayin da farashin kayayyaki ya kara hauhawa da kaso 3, baya ga rashin tabbas game da harkokin tattalin arziki, wanda matsalolin cinikayya da na siyasa a yankin suka haifar.
Ya ce a shirye kasashen yankin suke su ci gaba da fafutukar neman nasarori da ci gaba mai dorewa, duk da tangardar da ake gamuwa da su.
A cewar jami'an kungiyar, ana sa ran taron zai fitar da wasu dabarun da za su inganta dunkulewa da bunkasa huldar cinikayya tsakanin kasashe mambobin kungiyar. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China