Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamaru za ta yi zaben 'yan majalisu da kamsiloli a 9 ga Fabrairun 2020
2019-11-11 09:41:10        cri

Shugaban kasar Kamaru Paul Biya, ya sanya hannu kan wata doka a jiya Lahadi, wacce ta ayyana gudanar da zaben 'yan majalisar dokokin kasar da na kamsilolin kananan hukumomi a ranar 9 ga watan Fabrairun shekarar 2020.

Zabukan biyu wadanda aka dage ranakun gudanar da su har sau biyu sakamakon barazanar mayakan 'yan aware dake shiyyoyin kasar biyu masu magana da yaren Turanci da kuma hare haren mayakan 'yan ta'adda na Boko Haram a yankin arewa mai nisa na kasar.

Yan awaren sun yi baranazar hargitsa zabukan a shiyyoyin biyu masu fama da tashe tashen hankulla.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China