Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Fashewar tukunyar iskar gas ta halaka mutane 12 a Najeriya
2019-12-17 08:56:16        cri

Rahotanni daga Najeriya na cewa, a kalla mutane 12 ne suka gamu da ajalinsu a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina dake yankin arewa maso yammacin kasar, bayan da wata tukunyar iskar gas din dafa abinci ta yi bindiga.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina Isah Gambo ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, hadarin ya faru ne a ranar Asabar din da ta gabata.

Wata majiya daga wurin da lamarin ya faru, ta bayyana cewa, mata uku da yara biyar na daga cikin wadanda hadarin ya rutsa da su, kuma sun kone kurmus. An kuma yi jana'izarsu a ranar Lahadi.

Rundunar 'yan sandan jihar ta bayyana cewa, yanzu haka ta fara gudanar da bincike don gano abin da ya haddasa fashewar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China