Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An fara aiwatar da gangamin hade Rwanda da wayoyin salula
2019-12-24 10:34:56        cri

An fara aiwatar da wani gangamin gaggauta hade daukacin al'ummar kasar Rwanda da wayoyin salula na zamani. Gangamin wanda aka kaddamar a jiya Litinin, na da nufin gaggauta zamanantar da harkokin al'ummar kasar daidai da lokacin da ake ciki.

Kamfanin MTN na Afirka ta kudu reshen kasar Rwanda ne ya kaddamar da wannan gangami, ya kuma kunshi alkawarta rabawa al'ummar Rwanda dake sassa daban daban wayoyin salula har 1,100.

Da take karin haske game da hakan, yayin wani taron menema labarai da aka gudanar lokacin kaddamar da gangamin a birnin Kigali, fadar mulkin kasar, ministar fasahar sadarwar kasar Paula Ingabire, ta ce shirin hade Rwanda da wayoyin salula, na fatan daidaikun al'umma da kamfanoni, za su ba da gudummawa ga al'ummun da ba su mallaki wayoyin tafi da gidan ka ba.

Bugu da kari, ana sa ran gangamin zai samar da dama ga kamfanoni masu zaman kan su, da cibiyoyin gwamnatoci, da daidaikun mutane, ta yadda za su yi hadin gwiwa wajen sada daukacin 'yan Rwanda da wayoyin salula, da ma hidimomin yanar gizo da ake cin ajiyar su a dukkanin sassan duniya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China