Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin wadanda suka mutu a harin arewacin Rwanda ya kai 14
2019-10-07 16:18:36        cri

Jami'an 'yan sandan kasar Rwandan sun sanar a jiya Lahadi cewa, yawan mutanen da suka mutu a sanadiyyar harin da aka kaddamar a daren Juma'a a kusa da sanannen lambun shakatawar kasar wato Volcanoes National Park ya karu zuwa 14 bayan da wasu daga cikin wadanda suka samu raunuka suka mutu.

Wasu gungun mahara da ba'a san ko su wane ne ba masu dauke da makaman da suka hada da wukake da bindigogi ne suka afkawa kauyen Kinigi, dake gundumar Musanze a arewacin Rwanda, da misalin karfe 9:30 na daren Juma'a. kauyen Kinigi can ne helkwatar lambun shakatawa na Volcanoes National Park take, inda wasu dabbobin daji dake bakin karewa ke rayuwa kan tsauni.

Mutanen da suka samu raunuka suna samun kulawa a asibitin Ruhengeri dake gundumar Musanze, kakakin hukumar 'yan sandan yankin John Bosco Kabera ya sanar da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho.

Jami'an tsaro sun kashe mahara 19, kana sun cafke wasu 5 a kokarin da suke na zakulo maharan, a cewar sanarwar hukumar 'yan sandan da ta fitar tun da farko a ranar Lahadi.

Hukumar 'yan sandan ta bayyana harin da cewa, yana da rashin tausayi ne kasancewar maharan sun kashe wasu daga cikin mutanen kauyen a cikin gidajensu ta hanyar daba musu wuka.

Sai dai hukumar ta baiwa al'umma tabbacin maido da kwanciyar hankali a yankin, hukumar 'yan sandan tana ci gaba da sintiri domin farautar dukkan mutanen dake da hannu a harin.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China