Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin kasar Sin zai kammala ginin tashar wutar lantarki a Zambiya ya zuwa 2020
2019-07-15 10:16:10        cri

Gwamnatin Zambiya, ta ce ana sa ran kamfanin Sinohydro Corporation na kasar Sin, zai kammala aikin ginin tashar wutar lantarki ta Kafue Gorge, mai karfin megawatt 750 a badi.

Ta ce da zarar an kammala ginin tashar, karfin wutar lantarki da Zambia ke samarwa zai karu zuwa megawatt 3,750 daga megawatt 2,900.

Ministan makamashi na kasar Mathew Nkhuwa, ya ce aikin tashar wutar lantarki ta Kafue Gorge na tafiya kamar yadda aka tsara, kuma ana sa ran mika ta hannun gwamnatin kasar a shekarar 2020.

Ya kara da cewa, suna farin ciki da aikin da kamfanin kasar Sin ke gudanarwa, inda ya ce aikin ya kai matakin kaso 67 na kammaluwa.

Da yake ganawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a birnin Chingola, Ministan ya ce da zarar tashar ta fara aiki, Zambia za ta fara bayar da lantarki ga kasashen dake kudancin Afrika da ma sauran wasu sassan nahiyar.

A cewarsa, aikin ginin ya samar da guraben ayyukan yi sama da 3,000. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China