Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 37 sun mutu a zabtarewar kasa a Kenya
2019-11-24 15:14:40        cri
Mahukuntan kasar Kenya sun sanar a jiya Asabar cewa mutane 37 ne suka mutu a sanadiyyar ibtila'in zaftarewar kasa a yankin Pokot dake shiyyar arewa maso yammacin kasar bayan mamakon ruwan sama da aka sheka a daren Juma'a, kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka sanar.

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, ya aike da sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su, kana ya bada tabbacin ceto dukkan mutanen da suka bace tare daukar kwararan matakan rigakafin magance hasarar rayuakan jama'a a nan gaba.

Babban sakataren harkokin cikin gida na kasar Kenya, Fred Matiang'i ya ce, jami'an aikin ceto suna ci gaba da gudanar da ayyuka a kauyen da lamarin ya faru.

Matiang'i ya kara da cewa, gwamnati ta tura jami'an sojoji da 'yan sanda dauke da kayayyakin aiki domin gano dukkan mutanen da suka makale a cikin tabo.

A cewarsa, da farko yanayin tsananin zafi ya haifar da jinkiri wajen aikin ceto mutanen da ibtila'in ya shafa, ya kara da cewa, ana ci gaba da aikin tantance girman barnar da ibtila'in ya haddasa. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China