Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kenya na shirin soke biyan wasu haraji don bunkasa makamashi maras gurbata muhalli
2019-11-22 12:26:14        cri

Darektan hukumar daidaita farashin man fetur da iskar gas, makamashi da man fetur na kasar Kenya (EPRA) Edward Kinyua, ya bayyana cewa, kasarsa tana duba yiwuwar yin rangwame a harajin da ake biya a fannin man fetur da iskar gas, a wani mataki na bunkasa hanyoyin saukaka amfani da makamashi maras gurbata muhalli.

Ministan ya shaidawa wani taron dandali a Nairobi cewa, a halin yanzu hukumar tana tattaunawa da baitul malin kasa, don gano harajin da kananan masana'antun cikin gida dake samar da tukwanen iskar gas ba za su rika biya ba. Manufar ita ce, rage farashin tukwanen iskar gas din, ta yadda magidanta masu karamin karfi za su daina amfani da gawayi, iccen girki da man kalanzir yayin girke-girke.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China