Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kaddamar da sabbin matakan kyautata sassan makamashin Afrika
2019-06-06 11:10:53        cri
Hukumar raya tattalin arzikin Afrika ta MDD (ECA) ta sanar da cewa, shugabannin sassan makamashin bola jari na nahiyar Afrika da Turai sun kaddamar da wani sabon shiri, mai taken Afrika ta bola jari, da nufin bunkasa hanyoyin zuba jari a fannin makamashi irin na bola jari a nahiyar a yayin wani taron asiri.

A cewar hukumar ta ECA, sabon tsarin na Afrika ta bola jari wanda aka kaddamar, zai kasance wani sabon salo ne na kawo sauye sauye ta fuskar samar da makamashin bola jari a nan gaba.

Sanarwar ta ce, a matsayin wani sashe na sabon shirin, shugabannin kula da makamashin bola jari, suna kokarin neman yin hadin gwiwa a wannan fanni da nufin samar da kyakkyawan mahallin zuba jari a bangaren makamashin bola jari a Afrika.

Hukumar ECA ta ce, a gun taron din da ya mai da hankali kan makamashin bola jari, aka jaddada bukatar dake akwai wajen yin hadin gwiwa mai karfi tsakanin bangaren gwamnati da hukumomi masu zaman kansu a wannan fanni domin kafa tushe na kawo sauyi ga sha'anin bunkasa makamashin bola jari mai dorewa a nahiyar Afrika. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China