Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Habasha da Sin za su hada hannu wajen gina yankin masana'antu da darajarsa ta kai miliyan 300
2019-08-13 10:30:27        cri

Kasashen Sin da Habasha, sun shirya gina sabon yankin masana'antu da darajarsa ta kai dala miliyan 300, a kasar dake gabashin Afrika.

Jami'in dake kula da harkokin cinikayya da tattalin arziki na ofishin jakadancin Sin a Habasha, Liu Yu, ya shaidawa Xinhua cewa, za a fara ginin yankin masana'antun a birnin Adama dake da nisan kilomita 99 daga kudu maso yammacin birnin Addis Ababa, kafin karshen shekarar 2019.

Liu Yu, ya ce za a samar da kaso 85 na kudin ginin ne daga rancen kasar Sin mai rangwame, yayin da kaso 15 zai fito daga gwamnatin kasar Habasha.

Ya ce, yankin zai mayar da hankali kan jan hankalin kamfanoni masu kera kayayyakin aiki, yana mai cewa, yanzu haka an kammala aikin samu filin ginin da sauran shirye shiryen samar da kudin aiwatar da aikin.

Yankin zai zama irinsa na biyu, da ya samu kudin aiki da kwarewa daga kasar Sin a birnin Adama, wanda ke zaman cibiyar harkokin kasuwanci a yankin tsakiyar Habasha.

A watan Oktoban shekarar 2018 ne firaministan Habasha Abiy Ahmed, ya kaddamar da yankin masana'antun na farko na birnin Adama, wanda kamfanin gine-gine na kasar Sin wato CCECC, ya gina a kan kudi dala miliyan 146.

Ana sa ran yankin masana'antun na biyu da zai mamaye fili mai fadin kadada 100, zai samar da aikin yi ga 'yan kasar kimanin 25,000. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China