Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Najeriya sun kashe mayakan Boko Haram 10 a jihar Borno
2019-11-06 09:45:03        cri

Rahotanni daga Najeriya na cewa, sojojin kasar sun yi nasarar kashe mayakan Boko Haram 10, kana wasu da dama sun arce da raunin harbin bindiga a jikinsu, biyo bayan wani hari da sojojin suka dakile a jihar Borno dake yankin arewa maso gabashin kasar ranar Talata da safe.

Da yake karin haske kan lamarin, kwamandan sojojin kasa dake yankin arewa maso gabashin Najeriya, Bulama Biu, ya bayyana cewa, sojojin sun kuma yi nasarar kama wasu mayakan Boko Haram guda biyu, yayin wani musayar wuta da suka kwashe kimanin sa'o'i uku suna yi da 'yan ta'addan a kan hanyar Monguna-Ngolom-Marte.

Bayanai na cewa, wasu mayakan Boko Haram ne, suka yiwa sojojin da aka tura yankin na Marte dake jihar Borno kwanton bauna, inda suka kai musu hari da motoci masu dauke da bindigogin yaki, sai dai sojojin sun yi nasarar dakile wannan hari. A cewarsa, 'yan ta'addan na Boko Haram sun arce, saboda manyan makaman da sojojin suka yi amfani da su.

Ya ce, ko da a ranar Litinin da ta gabata, wasu mayakan Boko Haram, sun yi yunkurin kai wani hari a Gajiganna, dake jihar Borno, amma sojojin sun mayar da su baya, lamarin da ya tilastawa 'yan ta'addan ranta cikin na kare.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China