Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hatsarin mota yayi sanadin rayuka 6 tare da raunatar wasu 10 a Nijeriya
2019-09-25 09:46:18        cri
Wani hatsarin mota da sanyin safiyar jiya Talata, yayi sanadin mutuwar mutane 6 da raunatar wasu 10, a jihar Gombe dake arewa maso gabashin Nijeriya.

Mataimakin kwamishinan 'yan sandan jihar Gombe, Nasiru Mohammed, ya ce lamarin ya auku ne lokacin da wata babbar mota dauke da kayakin rufin gini, ya buge ababen hawa da dama, ciki har da babura da babura masu kafa 3 wato Keke Napep, akan wata gada dake kan titin Gombe zuwa Biu.

Nasiru Mohammed ya kara da cewa, ana samun karuwar aukuwar hatsari a titin a baya bayan nan.

Ya ce kwarya-kwaryan bincike ya nuna cewa babbar motar ta samu matsalar birki yayin aukuwar lamarin.

A cewar hukumomin kula da tituna a Nijeriya, rashin kyan tituna da tukin ganganci da daukar kaya ko fasinjoji fiye da kima, na daga cikin abubuwan dake haddasa hatsurra a kasar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China