Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Nigeria za ta kafa kotunan musammam domin gurfanar da masu hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba
2019-11-23 15:31:49        cri

Gwamnatin Nijeriya ta ce tana kokarin samar da kotunan musammam da za a rika gurfanar da masu hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba.

Ministan ma'adinai da karafa na kasar Uchechukwu Ogah, ya shaidawa manema labarai jiya a jihar Anambra dake kudu maso gabashin kasar cewa, za a kafa kotunan ne a kowace shiyya ta kasar, musammam domin tafiyar da shari'o'in da suka shafi hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba, wanda abu ne da ya zama ruwan dare.

A cewarsa, Nijeriya wadda ita ce kasa mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Afrika, na da albarkatun karkashin kasa sama da 25 dake da karfin da za su bunkasa tattalin arzikin kasar, ta yadda za ta kai ga cimma burinta na samu ci gaba.

Sai dai, hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba da cin hanci na daga cikin abubuwan dake mummunan tasiri kan ci gaban tattalin arzikin kasar.

Ministan ya ce gwamnatin kasar ba ta hana kowa shiga harkar hakar ma'adinai ba, manufarta ita ce a kiyaye ka'idoji sannan a mallaki lasisin hakar ma'adinai daga hukumomin da suka dace. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China