Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta kara samar da kudade don magance matsalar sauyin yanayi
2019-09-18 09:30:25        cri

Jami'i a ma'aikatar muhalli da yanayin muhallin halittu na kasar Sin Li Gao, ya bayyana kudirin kasarsa na kara samar da kudade ga shirye-shiryen tunkarar matsalar sauyin yanayi da hayaki mai gurbata muhalli da ake fitarwa.

Li ya ce wannan wani kyakkyawan mataki ne da kasar ta bullo da shi, a kokarin da take na samar da kudade don magance matsalar gurbatar muhalli.

A jawabin da ya gabatar a dandalin yaki da gurbatar muhalli, jami'in ya kuma yi kira ga kasashen duniya, da su karfafa alaka wajen samar da tallafin kudade don magance matsalar yanayi, ta yadda za a bunkasa aiwatar da ayyukan kare muhalli a ketare cikin hadin gwiwa.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China