2019-12-12 11:06:31 cri |
AU ta ce duk da irin ci gaba da ake samu a fannin raya tattalin arziki da jin dadin jama'a a nahiyar, har yanzu Afirka na da rauni game da tunkarar matsalolin sauyin yanayi, tana kuma gamuwa da bala'u daban daban masu nasaba da sauyin yanayi. Kaza lika wannan matsala na yin tarnaki ga burin cimma ajandar kasashenta nan da shekarar 2063, da ma kudurorin dake kunshe cikin shirin samar da ci gaba mai dorewa na kasa da kasa ko SDGs a takaice.
A baya bayan nan ma dai, bankin duniya ya fitar da wani rahoto, wanda ya bayyana irin yadda kasashen Afirka da dama suka cimma manyan nasarori cikin gwamman shekarun da suka shude, inda matsakaicin alkaluman ci gabansu ya karu da kaso 4.5 bisa dari, to sai dai kuma sauyin yanayi mai nasaba da karuwar zafi ko raguwarsa, da yanayin ruwa, da sauran bala'u masu aukuwa sakamakon hakan, na barazana ga wannan ci gaba.
Sanarwar ta AU ta ce, kungiyar na jaddada muhimmancin aiwatar da yarjejeniyoyin kasa da kasa na dakile tasirin sauyin yanayi, wadanda suka hada da yarjejeniyar Paris, da tsarin aiki na Sendai, da kudurorin wanzar da ci gaba na SDGs, da ajandar "New Urban". (Saminu Hassan)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China