Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban jami'in AU ya yaba da taimakon da Sin take baiwa rundunar ASF
2019-12-16 10:10:53        cri

Darektan sashen zaman lafiya da tsaro na hukumar zartaswar kungiyar tarayyar Afirka Admore Kambudzi, ya yaba da yadda kasar Sin da sauran abokan hulda na kasaahen waje suke taimakawa rundunar kwata kwana ta Afirka(ASF).

Admore ya bayyana haka ne yayin taron kwamitin kwararru na kungiyar AU karo 12 kan harkokin zaman kafiya da tsaro.

Jami'in ya bayyana wasu daga matakan da kungiyar mai mambobin kasashe 55 ke shirin bullo da su na ganin an daina jin amon bindigogi a sassan nahiyar, yana mai jaddada cewa, manufar galibin wadannan matakai ita ce, raya da karfafa manufofi, da tsare-tsare, da dabaru da albarkatun da za su taimaka wajen saurin tura rundunar a lokacin da bukatar hakan ta taso.

Ya ce, wasu daga kasashe mambobin kungiyar, sun kara samar da kudade kamar yadda hukumar zartarwas kungiyar ta bukata, ciki har da jigilar dakarun ta jiragen sama. A nasu bangaren abokan hulda kamar Sin da Turkiya sun samar wa rundunar kwata kwana ta Afirka(ASF) kayan aiki, ta yadda za ta gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China