Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU na fatan hada gwiwa da Sin wajen dakile matsalolin karancin abinci bayan kaka a Afirka
2019-09-18 19:27:28        cri

Kungiyar tarayyar Afirka ta AU, ta sha alwashin kara hadin gwiwa da kasar Sin, wajen dakile matsalolin karancin abinci dake biyo bayan lokacin kaka a kasashen dake nahiyar Afirka.

Da take bayyana hakan ga manema labarai a gefen taro na 2, na nazartar kalubalen karancin abinci bayan kaka, da baje kolin kayayyaki masu nasaba da hakan, shugabar sashen raya tattalin arzikin yankunan karkara, da ayyukan gona a kungiyar ta AU Janet Edeme, ta ce daukacin kasashe mambobin AU 55, na fatan karfafa hadin kai da Sin, domin rage tasirin wannan matsala.

Janet Edeme, ta bayyana hakan ne a jiya Talata, a helkwatar kungiyar ta AU dake birnin Addis Ababan kasar Habasha. Ta ce a farkon wannan wata, AU da kasar Sin sun sanya hannu kan takardar fahimtar juna, da nufin karfafa hadin gwiwa a sassan tsaron abinci, da ingancin sa, da kare hasarar abincin.

Edeme ta kara da cewa, nahiyar Afirka na fatan amfana daga fasahohin kasar Sin na kare karancin abinci bayan lokacin kaka. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China