Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An samu gaggarumin ci gaba wajen yaki da cutar sida a fadin duniya
2019-12-01 17:24:07        cri

Gabannin ranar yaki da cutar AIDS wato ranar 1 ga watan Disamba, shirin yaki da cutar AIDS ta Majalisar Dinkin Duniya ya bullo da wani sabon rahoton dake nuna cewa, an cimma tudun dafawa wajen yaki da cutar a duk fadin duniya, sai dai har yanzu cutar na zama wata babbar matsala da take ciwa wasu kasashe tuwo a kwarya a fannin kiwon lafiya, musamman kasashen nahiyar Afirka.

A cewar rahoton, an samu babban ci gaba a fannonin da suka shafi rage adadin mutanen da suka kamu da cutar kanjamau da jinyarsu. Alal misali, daga shekara ta 2010 zuwa ta 2018, a yankunan gabashi da kudancin nahiyar Afirka inda cutar kanjamau ta fi Kamari, adadin sabbin mutanen da suka kamu da cutar ya ragu da kaso 28.

Akwai muhimman dalilan da suka sa aka samu dimbin nasarori a fannin yaki da cutar kanjamau a duniya, inda shirin yaki da cutar AIDS ta MDD ya yaba da gudummawar da al'ummomi suka bayar. Amma shirin ya ce har yanzu ana fuskantar wasu manyan kalubale, inda a shekara ta 2018, a kara samun mutane miliyan 1.7 da suka kamu da cutar a duniya, musamman a nahiyar Afirka. Kididdiga daga hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO ta nuna cewa, a shekarar da muke ciki, yawan mutanen da suka kamu da cutar sida ya kai kimanin miliyan 37.9, ciki hadda kimanin miliyan 25.7 dake zaune a kasashen Afirka.

Rahoton ya kuma bukaci kasashe daban-daban su goyi bayan kungiyoyin al'umma da ke yaki da cutar AIDS a unguwanni, inda ya ce, matukar aka ba kungiyoyin al'umma a unguwanni cikakken goyon-baya, za'a cimma burin kawo karshen yaduwar cutar AIDS a duniya baki daya.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China