Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban titin da Sin ta gina zai inganta cinikayya da tattalin arzikin Habasha
2019-06-19 10:10:47        cri

Gwamnatin Habasha ta ce, sabon babban titin da kasar Sin ta gina mai tsawon km 220 da ya hada kasar da ba ta da iyaka da teku, da tashar jirgin ruwa na kasar Djibouti, zai biya bukatun shige da ficen kayayyaki dake karuwa a Habashar.

Da yake ganawa da wakilin Xinhua, daraktan sashen wayar da kai na hukumar kula da tituna ta Habasha ERA, Samson Wondimu, ya ce yanzu kasar Djibouti ce ke kula da kaso 95 na harkokin cinikayyar da suka shafi shige da ficen kayayyaki daga Habasha, kuma titin da darajarsa ta kai birr biliyan 5.2, kwatankwacin dala miliyan 179, zai kara bunkasa ci gaban tattalin arzikin kasar.

A matsayinta na daya daga cikin kasashen da suke hadin gwiwa da kasar Sin wajen aiwatar da shawarar Ziri Daya da Hanya Daya (BRI), Habasha ta cimma aiwatar da manyan ayyukan raya kasa daban-daban, ciki har da layin dogo mai amfani da lantarki wanda ke zirga zirga tsakanin kasa da kasa, da ya hada Addis Ababa, babban birnin kasar da kasar Djibouti.

Costantinos Bt. Costantinos, wanda ya taba zama mai ba da shawara kan tattalin arziki ga Tarayyar Afrika AU da hukumar kula da tattalin arzikin nahiyar Afrika ta MDD ECA, ya shaidawa Xinhua cewa, a matsayinta na daya daga cikin kasashe na farko da suka hada hannu da kasar Sin karkashin shawarar BRI, Habasha na ganin kyawawan sakamakon hadin gwiwarta da kasar ta Sin.(Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China