Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin:Ana nuna wa musulmi wariya a Amurka
2019-12-10 20:31:52        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Hua Chunying ta bayyana cewa, kaso 75 na musulmi baligai dake Amurka na fuskantar nuna wariya. Hakan na nufin cewa, al'ummomin kasa da kasa na da hujjar nuna damuwa game da manufofin Amurka kan al'ummar musulman dake zaune a cikin kasar, ciki har da yanayin kare hakkin musulman a kasar ta Amurka.

Madam Hua ta bayyana cewa, wasu mutane a Amurka suna nuna damuwa babu gaira babu dalili kan kabilar Uygur dake Xinjiang, amma sun manta cewa, Amurka ce kasa daya tilo a duniya da ta haramta "Mu" musamman kungiyoyin musulmi. A 'yan shekarun nan, kasar Amurka ta tayar da yake-yake a kasashen Iraki da Syria, da Libya da Afghanistan da wasu kasashe, bisa hujjar yaki da ta'addanci, matakin da ya rutsa da miliyoyin fararen hula da ba su san hawa ba balle sauka, kuma dukkan kasashen da wannan lamari ya shafa, kasashen musulmi ne.

Bugu da kari, Hua Chunying ta jaddada cewa, Uygur, na daga cikin kananan kabilu 56 na kasar Sin. Don haka, su da ragowar kabilun kasar 55, kan su a hade yake, inda suke rayuwa cikin 'yanci da farin ciki da yanayi mai kyau kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

Ta ce, kasar Sin tana da alaka mai kyau da galibin kasashen musulmi. Don haka, ba abin mamaki ba ne cewa, Amurka tana kishi da wadannan kasashe, amma kuma, kasar Sin ba za ta taba amincewa, Amurka ta rika yada jita-jita da ma kokarin neman shafa mata kashin kaza ba.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China