Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na fatan Amurka za ta saurari ra'ayin masu hangen nesa
2019-12-10 19:27:06        cri

Kwanan baya wasu masanan Amurka sun yi tsokaci kan ci gaban kasar Sin a wurare daban daban, sannan suka soki manufar gwamnatin Trump kan kasar Sin.

Tsohon mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka Robert Zoellick ya bayyana cewa, takaddamar dake tsakanin Sin da Amurka za ta kawo hasara da hadari ga sassan biyu. Darektan cibiyar nazarin dauwamammen ci gaba ta jami'ar Columbia ta Amurka Jeffrey D. Sachs ya nuna cewa, ya dace kasar Sin ta yi kokarin samun ci gabanta, kana bai kamata ba Amurka ta tayar da takaddamar cinikayya da kasar Sin.

Kan wannan batu, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana cewa, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, wasu Amurkawa suna shafawa kasar Sin kashin kaza, har sun zargi jam'iyyar dake mulki a kasar da ma tsarin kasa na kasar Sin, duk wadannan ba ma kawai sun sa hankalin Sinawa ya tashi ba, har ma sun sa masu hangen nesa na bangarori daban daban na Amurka su ma ba su ji dadi ba, a don haka kasar Sin tana fatan Amurka za ta saurari ra'ayoyin da masu hangen nesa suka fada, ta hada kai tare da kasar Sin, ta yadda za su ingiza ci gaban huldar dake tsakanin sassan biyu gaba cikin lumana.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China